Yadda Taron Manema Labarai Ya Gudana a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina Kan Ziyarar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Za a Yi a Ranar 2 ga Mayu, 2025

 A


n gudanar da taron manema labarai a fadar Gidan Gwamnatin Jihar Katsina a ranar Laraba, 30 ga Afrilu, 2025, karkashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Katsina, Dr. Bala Salisu Zango. Taron ya mayar da hankali kan bayani dalla-dalla game da ziyarar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai kai jihar Katsina a ranar Juma’a, 2 ga Mayu, 2025.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai, Shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Aikin Jarida (NUJ) na jihar, da sauran masu ruwa da tsaki a fannin watsa labarai.

A yayin taron, Kwamishinan Yaɗa Labarai ya bayyana cewa ziyarar shugaban ƙasa na da nufin duba manyan ayyukan ci gaba da Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda ta aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata. Cikin ayyukan da za a ziyarta akwai: gina hanyoyi, inganta fannin kiwon lafiya, habaka ilimi, noma da kiwo, da kuma shirye-shiryen tallafawa masu ƙaramin ƙarfi da raya garuruwa.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, shugaban ƙasar zai ƙaddamar da wasu daga cikin muhimman ayyukan gwamnati yayin ziyarar tasa, wanda ke nuna haɗin kai da goyon baya ga cigaban jihar Katsina.

No comments: