An gudanar da babban taron baje kolin ƙere-ƙere da hazaƙa karo na biyu (2.0) da aka laƙaba masa suna Arewa Tech Festival a jihar Katsina.


 A ranar Laraba, 21 ga watan Mayu, 2025 ne aka gudanar da wannan baje koli a cibiyar Continental Support and Event Centre da ke bayan Katsina City Mall a cikin birnin Katsina.

Daga cikin fitattun baƙin da suka yi jawabi a wajen taron har da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, wanda Sakataran Gwamnatin Jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari, ya wakilta.

Haka kuma, Ministan Sadarwa, Dakta Bosun Tijani, shugaban hukumar kididdiga ta Katsina, Naufal Ahmad, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i, tare da wakilin Gwamnan Jihar Zamfara da wasu muhimman baki sun halarci taron.

Wannan baje koli ya ja hankalin mahalarta daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.

No comments: