A wani mataki na karfafa harkar lafiya da saukaka wa al'umma samun kulawa ta gaggawa da nagarta, Gwamnan jahar katsina malam Dikko Umar Radda ya bada umarnin ygaran Asibitoci biyu biyu a kowacce karamar hukumar cikin jihar katsina.
Wannan Tsarin na nufin gyaran Asibitoci guda 68 a duk fadin jihar wani muhimmin sauyi da zai kawo sauki wahalar da jama'a ke fuskanta wajan samun kiwon lafiya, musamman a matakin kasa.
Wannan sabon shiri yana daga cikin manufofin Gwamnatin Radda na tabbatar da cewa kowane dan jihar katsina yana da damar samun kulawa ta lafiya ba tare da wahala ko tafiye tafiye masu nisa ba. Gwamna ya ce kiwon lafiyar al'umma ce kuma babu ci gaba idan ba a kula da lafiya ba.
Wannan matakin zai taimaka wajena.
Samar da ingantattun kayan aiki a Asibitoci.
Gina da gyaran gine gine na zamani.
Koyar da maaikata da inganta kwarewarsu.
Karfafa rigakafi da magani a matakin farko.
Gwamna Radda na ci gaba da nuna kishin al'umma ta hanyar sauya fasalin rayuwa da gine ginen more rayuwa dukkan sassa na jihar katsina wannan sabon mataki a fannin lafiya na nuna jajircewasa wajan gina sabuwar katsina mai cike da kwanciyar hankali da jin dadi
No comments:
Post a Comment