MAI MAGANA DA YAWUN GWAMNA JIHAR KATSINA IBRAHIM KULA MUHAMMAD YA BAYYANA CEWA

 Majalissar zartarwar jahar katsina ta amince da kafa kananan cibiyoyin harhada kayan aikin gona na zamani wato mini agricultural mechanization centrel a dukkan kananan hukomomi 34na jihar

a


mincewar ta biyo bayan taro da gwamna dikko Umar radda ya jagoranta a dare talata a gidan Gwamnati.

Da yake zantawa da manema labarai a larabar nan kwamishinan Harkokin noma da bunkasa Harkokin noma da bunkasa kiwo farfesa AHMAD MUHAMMADU BAKORI ,ya bayyana cewa kowace cibiya zata samu taraktoci 10, wanda jimilla zai kai taraktoci 340 da za a raba a fadin jihar

Biyo bayan k'addamar da cibiyar harhada kayan aikin gona na zamani ta jihar katsina da shugaban kasa yayi a ranar 2 ga mayu majalisar ta amince da kafa wadannan kananan cibiyoyi daza su kunshi ganin ofisoshi, wuraren gyaran na'urori,da wuraren ajiye taraktoci da kayan aiki, inji farfesa bakori 

Farfesa bakori ya jadda cewa taraktocin ba na siyarwa bane za a sarrafa sune ta hanyar hadin gwiwar Gwamnati da masu zaman kansu wato tsarin PPP.

muna rokon jama'a dasu guji Kiran ko matsa wa jami'an gwamnati lamba don samun taraktoci. Maimakon haka duk manomi mai sha'awar amfani da tarakta yaje cibiyar da aka kafa ta karamar hukumarsa ya mika bukatarsa tare da bayyana girman gonar dai noma, inji kwamishinan,

No comments: