A ranar Talata 29 Afrilu 2025, Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta tattauna kudirin da ke neman magance matsalar karancin ruwa a Karamar Hukumar Faskari. Kudirin ya fito ne daga Dr. Sama’ila Mu’azu Bawa, dan majalisar da ke wakiltar Mazabar Faskari.
Hon. Sama’ila Bawa ya jaddada cewa matsalar karancin ruwa a yankin na kara ta'azzara, yana mai kira ga gwamnatin jiha da sauran hukumomi su dauki matakin gaggawa don ceto rayukan al’umma.
A wani bangare na zaman, Hon. Salisu Hamza Rimaye, Shugaban Kwamitin Gudanarwa, ya gabatar da rahoton kwamitinsu kan kudirin doka da zai tanadi wa'adin shugabannin hukumomi (Parastatals) a cikin jihar. Wannan kudiri na da nufin tabbatar da sahihanci da inganci a tsarin shugabanci da gudanar da ayyuka a hukumomin gwamnati.
Haka kuma, Hon. Lawal Abdu Ibrahim, Shugaban Kwamitin Shari'a, Alkalai da Hakkin Dan Adam, ya gabatar da rahoton kwamitinsu kan kudirin sauya dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka ta Jihar Katsina, 2021. Kudirin yana da nufin inganta tsarin shari’a domin tabbatar da adalci da kare hakkin dan Adam a fadin jihar.
✍️✍️Yusuf Hamza Dutsi.
No comments:
Post a Comment