Wađannan matan an đauko su ne daga ķananun hukumomi 34 da suke a fađin jihar ta Katsina.
Sannan kowacce mace an bata buhun shinkafa wanda nauyin shi ya kai 25kg, tare da Naira dubu goma-goma 10,000.
Malam Dikko Radda, a jawabin nashi ya yaba kwarai da irin ķoķarin da sauran muķarraban shi sukeyi babu dare babu rana domin ciyar da jihar katsina dama al'ummar jihar gaba.
Rađđa ya buķaci wađanda suka amfana da tallafin da su tabbata cewa sunyi amfani da tallafin ta hanyar da ta dace.
Dikko Radda ya bugi ķirji inda yace "a gwamnatance a gwada mana waya fimu yin hanyoyi, kwalbatici gina Asibiti da kuma gina makarantu, hanyoyi tare da tallafawa al'umma? Bama Katsina kađai ba kaf Nigeria idan akwai, a gayaman".
Daga ķarshe yayi addu'ah ga ilahirin al'ummar da suka halarci wannan taron dama sauran al'umma na gida tare da fatan Allah ya maidan kowa gidan shi lafiya.
No comments:
Post a Comment