A
wani zama da aka gudanar yau Laraba, 9 Afrilu 2025, karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, majalisar zartarwa ta amince da a fara aikin gyaran dam ɗin da ke garin Sabuwa ba tare da bata lokaci ba.
Majalisar ta bayyana cewa aikin za a kammala shi cikin kwanaki 90 daga ranar da aka fara aikin, domin tabbatar da ingancin ruwa da amfanin gona ga al’ummar yankin.
Bugu da ķari majalisar ta ķara bayyana aikin wannan Dam a matsayin wata gagarumar hanyar kawoma yankin cigaba ta fannoni daban-daban, kamar haka; za'a samu rubanyar al'ummar da suke yin noman rani da kuma isasshen ruwan sha kuma mai tsafta a garin da kuma maķwabtan su.
No comments:
Post a Comment