A
ranar Talata 8 ga watan Afrilu na 2025, Tawagar ƙungiyar gwamnonin Najeriya ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Kwara Abdulrazaq Abdulrahman, suka ziyarci gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, domin yi mashi ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar shi.
Da yake gabatar da jawabin ta'aziyyar Gwamnan Jihar ta Kwara kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin Abdulrazaq Abdulrahman, ya bayyana rashin mahaifiyar gwamnan Hajiya Safara'u Umaru Raɗɗa tana da shekaru 93, a matsayin babban rashi , wanda ba'a iya maye gurbin shi.
Sabo da haka ne muke miƙa ta'aziyyar mu a madadin gwamnonin Najeriya, ya kuma yin addu'ar Allah SWT ya jikan ta da rahama, ya sanya aljanna fiddausi ce makomar ta.
A ɗaya ɓangaren Mataimakin gwamnan jihar Katsina Hon. Faruk Lawal Joɓe, ya yi jawabi a madadin gwamna Raɗɗa, inda ya bayyana tun da akayi rasuwar ake samun ɗaiɗaikun gwamnoni daga jihohi daban-daban da suka riƙa zuwa yin ta'aziyyar wannan rashi.
Ya kuma ce akwai da yawa wanda suka yi mashi ta'aziyyar a ƙasa mai tsarki kafin dawowar shi gida kuma bayan sun dawo gida suka zo tare da iyalan su domin ƙara yi mana gaisuwa , bugu da ƙari gwamnonin jihar Kano da Jigawa Injiniya Abba Kabir Yusuf, da takwaran shi Umar Sulaiman Namadi Ɗan-modi da su akayi jana'izar marigayiyar.
Sabo da haka a madadin gwamna Raɗɗa da ɗaukacin al'ummar jihar Katsina muna miƙa godiyar mu bisa wannan karamci da aka yi mana a lokacin wannan rasuwa.
Tawagar gwamnonin ta ƙunshi gwamnan jihar Kogi Ahmed Usman Ododo, na jihar Ekiti Biodun Oyebanji, sai na jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa.
No comments:
Post a Comment