A ranar Asabar 19 Afrilu 2025, Hon. Hamza Sulaiman Faskari ya amshi tuta a hannun mai martaba Sarkin Daura Dr. Umar Faruq Umar, inda ya nađa shi Sarautar Sadaukin Kasar Hausa na 1 tun tarihin kafuwar masarautar Daura (asalin tushen Hausa bakwai).
Hamza Faskari shine Kwamishinan muhalli na jihar Katsina kuma Wamban Faskari.
A lokacin da mai martaba Sarki yake bashi tuta ya jinjina ma Hamza bisa ga ķoķarin da yake yi babu dare babu rana domin ganin al'umma sun rayu cikin "yanci.
Sarkin ya ķara da cewa abun al'khairin da yake yi ma al'umma shi yake bibiyar shi har gashi yau Allah yasa ya zamo Sadaukin Ķasar Hausa na 1.
Daga ķarshe Sadauki ya miķa saķon godiya ga masarautar Daura da ta nađa shi wannan babbar sarauta ta Sadaukin Kasar Hausa, sannan ya jinjina ma al'ummar da suka zo na kusa dana nesa da ma wađanda Allah bai basu damar halartar taron nađin ba, musamman baķin da suka zo daga garuruwan nesa.
Daga ķarshe yayi ma kowa fatan Allah yasa ya koma gida lafiya, cikin aminci.
No comments:
Post a Comment