Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Lawal ya gudanar da taron manema labarai na wata-wata karo na biyar da aka gudanar a ranar Talata, 22 ga Afrilu, 2025.

 


Yayin da yake bayani kan gagarumar nasarar da Gwamna Dikko Umaru Radda ya samu a fannin filaye da tsare-tsaren gine-gine, Mataimakin Gwamnan ya ce: “Zuba jari da Gwamnati ta yi a KATGIS ya hada da kirkirar wata na’urar kwamfuta (software) ta musamman, da sayen kayan aiki (hardware), da kuma sayen takardar amintacciya daga Hukumar Tsaro da Bugawa ta Najeriya (NSPMC) don samar da Takardar Mallakar Fili (C of O)."

Malam Jobe ya bayyana cewa, kafa KATGIS “ya zama dole domin barin tsohuwar hanyar aikin hannu wajen rajistar filaye, wadda ke da wahala kuma ana iya yin magudi da damfara a cikinta, zuwa tsarin zamani da ke amfani da fasaha wanda ya fi sauri, gaskiya, da kuma saukaka adana bayanan filaye, wanda hakan zai rage rigingimu tsakanin masu filaye kuma ya karfafa samun kudaden shiga.”

Dangane da tasirin gagarumin ci gaban birane, Malam Jobe ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta biya diyyar filaye da dama da aka kwace don aiwatar da ayyukan raya kasa.

Wannan gwamnatin ta biya diyya da ta kai jimillar Naira biliyan 3,173,933,922.00 ga mutanen da aka shafa da kwace filaye don bada dama ga ayyukan raya kasa kamar gina sabbin hanyoyi, fadada makarantu, asibitoci, kasuwanni da sauran muhimman gine-gine a fadin jihar,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “An ware Naira biliyan 2 a kasafin kudin bana don ci gaba da biyan diyya ga mutanen da ayyukan gina sabbin gine-gine ke shafa.”

Yayin da yake bayani kan matakan karfafa doka da oda wajen gine-gine, Malam Jobe ya bayyana cewa, “An kashe Naira miliyan 725 wajen siyo manyan injinan aiki irin su Pay Loaders, Excavators, Tippers, Motocin Hilux da Babura domin sa ido kan ayyukan gine-gine tare da tabbatar da bin dokokin gine-gine yadda ya kamata.”

Ya ce, “Yawan karuwar jama’a da sauri yana kara jefa Gwamnati cikin kalubale da ke bukatar daukar mataki tun da wuri domin tabbatar da dorewar cigaba nan gaba.”

“Gwamnati ta yi manyan zuba jari don shiryawa karuwar birane da ake sa ran samu, ciki har da inganta tsarin gudanar da filaye, shirya sabbin tsare-tsaren gine-gine na birane, da kuma siyan kayayyakin aiki masu nauyi don tsare-tsaren gine-gine,” in ji shi.

Game da shirin tsara birane, ya ce: “Domin komawa tsarin amfani da taswirar birane wajen gina jiha yadda ya dace, mun zuba Naira miliyan 315,375 don sake duba Tsare-Tsaren Gine-Ginen Katsina, Funtua, da Daura daga shekarar 2025 zuwa 2040.”

Ya bayyana cewa wadannan taswirar gine-gine, tare da guda hudu – Dutsin-Ma, Malumfashi, Mani da Kankiya – “asalin wata kamfani ce daga Birtaniya mai suna Max Lock ta tsara su tun a shekarun 1970, kuma sun dade suna bukatar sabuntawa tun kusan shekaru 25 da suka wuce.”

Gwamnati ta kammala shirye-shiryen sake duba sauran taswirar hudu daga bana, tare da shirin kirkirar sabbin tsare-tsaren gine-gine ga sauran birane nan da shekarar 2026,” in ji Malam Jobe.

Taron manema labaran na wata-wata wanda aka fara a watan Nuwamba, 2024, na daga cikin hanyoyin tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen amfani da dukiyoyin al’umma, da kuma sanar da ‘yan kasa halin da ake ciki dangane da ci gaban jihar.


No comments: