Sarkin Malamai Abdulkarim Modubbo Ya Tallafawa Matasa da Marayu a Wani Gagarumin Taro a Katsina


A wani babban taro da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar Katsina, Sarkin Malamai na Magajin Gari, Abdulkarim Modubbo, ya bayar da gudummawa ta musamman domin tallafawa matasa da marayu tare da karfafa masu aikin yada sahihan ayyukan gwamnati.

Taron ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na jihar, ciki har da Dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Katsina, Hon. Ali Abu Albaba, shugaban hukumar tsaftace muhalli, Hon. Kabir Usman Amoga, manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, limamai da malamai, Sarkin Sharifai, Hajiya Rukayya Radda, da kuma zababben shugaban karamar hukumar Katsina, Hon. Isa Miqidad AD Saude.

A yayin taron, Hon. Abdulkarim Modubbo ya bai wa matasa masu yada manufofin gwamnati tallafin kudi har naira dubu goma-goma (₦10,000) kowanne. Haka zalika, ya tallafa wa marayu guda ashirin (20) da kayan more rayuwa. Bugu da kari, ya raba lambobin yabo ga wasu daga cikin membobin kafafen yada labarai, musamman 'Sarkin Malamai Media Team', domin yabawa da jajircewarsu wajen yada sahihan ayyukan Gwamna Malam Dikko Umar Radda.

Taron ya nuna yadda hadin kai tsakanin shugabanni da al’umma ke kara karfafa cigaba da wanzar da zaman lafiya a jihar Katsina.

No comments: