A
ranar alhamis 24- 05- 2025 shugabanin jamaiyyar APC matakin karamar hukumar suka shirya taron Taya murnar ga shugaban karamar hukumar a sakatariyar karamar hukumar Dake ciki garin Rimi.
Da yake gabatar da jawabin sa shugaban jamaiyyar APC na Abdullahi makurda ya fara da godiya ga Allah da ya nuna masa wannan rana wadda sukazo domin Taya murna ga shugaban karamar hukumar su.
Bisa ga zama shugaban karamar hukumar Rimi wanda suke alfahari dashi dashi shine sukaga ya dace su shirya masa wannan taro na taya murna matsayin sa na kula da jamiyya tun kafin samun wannan dama.
Shima a nasa jawabin shugaban karamar hukumar Rimi Hon Muhammadu Ali Rimi yayi godiya ga Allah da Kuma shugabancin jamaiyyar APC na karamar hukumar Rimi bisa shirya masa wannan taro.
Wanda a duk jahar katsina karamar hukumar Rimi ne kadai shugaban karamar hukumar wannan taro na taya murna.
Tabbas wannan abun yabawa ne Kuma hakan ya nuna akwai kyakkywar alaka tsakani, kuma in sha Allah za'a cigaba da tafiya tare domin kawo ma karamar hukumar cigaba.
Mutane da dama ne suka gabatar da jawabi na fatan alkhairi a wurin taron wanda suka hada shugaban masu ruwa da tsaki na karamar hukumar wanda ya samu wakilcin Hon Nasir Ala iyatawa, Alh. Tanimu maigari Alh. Saluhu majen Gobir da dai sauran su.
No comments:
Post a Comment