HAjj 2025||Gwamna Radda ya k'addamar da tawagar jihar katsina zuwa kasa mai tsarki

 G



wamna jahar katsina malam Dikko Umar Radda, ya k'addamar da tawagar da zata jagoranci aikin hajjin bana, inda ya nada mataimakinsa malam Faruq Lawal jobe, a matsayin Amirul Hajj.

Tawagar ta kunshi kakakin majalissar jihar katsina Nasir yahaya Daura wakilai daga majalissar masarautar Daura katsina da kwamishina Harkokin Addinai Alh. Shehu Abubakar Dabai, da wasu jamia'n gwamnati da malamai.

Gwamna Radda ya bukaci tawagar da su sa ido kan dukkan ayyuka da tsare tsaren da suka shafi jin dadin maniyyata sauka da tashi su, da kuma dawo da su gida lafiya.

Ya ja kunnan malamai da aka dauka daga kananan hukomomi da su gudanar da waazi cikin gaskiya yana mai  cewa Gwamnati ta kashe kudin jama'a wajan daukarsu don haka ana bukatar suyi aiki da rikon Amana.

Haka kuma ya umarci hukumar aikin hajjin da ta tabbatar da cewa duk ma aikatan da aka dauka sun sauke nauyi da aka dora masu, tare da daukar mataki kan wadanda basu ciki aiki ba.

A jawabin sa na godiya Amirul Hajj kuma mataimakin Gwamna malam Faruq Lawal jobe ya tabbatar da cewa tawagar za tayi duk mai yiwuwa wajan ganin an gudanar da aikin hajjin bana cikin nasara da tsari.

Ya kuma roki Allah daya basu nasara a cikin aikin hajjin na shekarar 2025.

No comments: