A ranar laraba 29 ga watan Janairu 2025 Dan takarar shugabancin karamar hukumar katsina a jam' iyyar APC HON ISAH MIQDAD AD SAUDE tare da sauran masu ruwa da tsaki na karamar hukumar katsina suka jagoranci mika tutar yakin neman zaben a filin Kangiwa dake ƙofar soro
Kwamishina ma' aikatar ruwa na jihar katsina HON BASHIR GAMBO SAULAWA shine ya jagoranci kwamitin masu ruwa da tsaki domin mika tutocin yakin neman zaben a filin kangiy dake kofar soro da yake gabatar da jawabi bayan kammala basu tutocin Dan takarar shugabancin karamar hukumar ta katsina HON.ISAH MIQDAD AD SAUDE ya fara da mika sakon godiya ga illahirin masu ruwa da tsaki na karamar hukumar katsina wanda suka halarta
Dama Wanda basu samu damar zuwa ba bisa irin taimakon da kuma gudunmawar da suke basu ya kuma roki al' ummar karamar hukumar katsina dasu fito ranar zaben
Ya kuma yin kira ga Al'umma na ƙaramar hukumar ta Katsina da fito domin maida biki musanman duba da la'akari da irin ayyukan da maigirma Gwamana jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya aiwatar A jihar Katsina
No comments:
Post a Comment