Malam Faruq Lawal Jobe ya gabatar da taron manema labarai na wata-wata a ofishinsa da ke tsohuwar gidan gwamnatin Jihar Katsina.a
A yayin taron, ya jaddada cewa gwamnatin Jihar Katsina ta mayar da hankali kan ci gaban ilimi, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda ta dukufa wajen inganta ilimi domin samar da ingantacciyar makoma ga al'ummar jihar.
Ya kara da cewa tun daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu, gwamnati ta zuba jari mai yawa don tabbatar da ingancin koyo da koyarwa. A cewarsa, gwamnatin ta kashe biliyan N9.1 ta hannun Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Katsina (SUBEB) domin gina sabbin ajujuwa 160 da gyara 258. Haka nan, an samar da rijiyoyin burtsatse 81, bandaki 46, tare da gidajen malamai 20. Bugu da kari, an samar da kujerun malamai 612 da kuma kujerun dalibai 14,602.
Mataimakin gwamnan ya kuma bayyana cewa an kashe biliyan N5.6 karkashin shirin TIS domin gina sabbin makarantu 150 tare da samar da wutar lantarki ta hasken rana, rijiyoyin burtsatse, da kuma kayan koyarwa.
No comments:
Post a Comment