Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, ya bayyana haka ne, a ranar Litinin 05/05/2025, a lokacin da yake ƙaddamar da fara siyar da takin zamani ga manoman jihar Katsina, na damunar bana wanda yawan shi ya kai tan 20,000 a ƙaramar hukumar Kusada.
Da yake gabatar da jawabi gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, ya shaida ma al'ummar jihar Katsina cewa " irin wannan tallafin da muka samar a damunar bara ya bunƙasa amfanin gona sosai ga manoma.
Ya ƙara da cewa kamar yadda nayi alƙawarin bayar da takin zamani na damunar bana kafin saukar ruwan sama, cikin ikon Allah yau na cika wannan alƙawari, domin inganta noma da wadatar da abinci a jihar Katsina, kuma ina kira ga manoman da su riƙa amfani da dabarun noma na zamani domin bunƙasa noma.
Ya cigaba da cewa zamu kai wannan taki ne a kowace rumfar zaɓe da ke wannan jihar, kuma za'a siyar da takin a farashi mai sauƙi na rabin kuɗin da ake siyar da shi a kasuwa.
Gwamnan yace bayan takin zamani da zamu raba wanda ya kai buhu 400,000, kwana biyu da ya gabata shugaban ƙasa Asiwaju Bola Tinubu, ya ƙaddamar da cibiyar samar da kayan aikin gona mai ɗauke da taraktoci 400 da sauran kayan aikin na zamani kuma kowace ƙaramar hukuma zata amfana da taraktocin nan.
Ya cigaba da cewa wannan taraktoci za'a riƙa bada su haya ne ga manoma, kowane manomi zai amshi haya, idan ya kammala amfani da ita sai ya dawo da ita, kuma mun yi hakan ne domin kauce ma abun da ke faruwa a baya wasu manya su handame ko a siyar da su wata jiha.
Daga ƙarshe Gwamnan ya bayyana irin muhimman ayyukan da yayi a jihar Katsina domin kawo cigaba a jihar, wanda suka haɗa da bunƙasa cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko, ilimi, magance matsalar tsaro, da sauran su.
A jawabin shi Kwamishinan gona na jihar Katsina Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, ya bayyana gwamnan jihar Katsina ya samar da takin ne domin inganta noma a jihar Katsina.
Ya cigaba da cewa noman damuna shine noman da al'ummar jihar Katsina suka fi dogaro da shi, sabo da haka wannan takin zai bada gagarumar gudummuwa domin cigaban noma, kuma wannan yinƙurin yana daga cikin ƙoƙarin gwamna na bunƙasa noma.
Tun da fari shugaban ƙaramar hukumar Kusada Hon. Sani Aminu Dangamau, ne ya fara jawabin maraba, inda ya bayyana kawo ƙaddamar da takin ƙaramar hukumar shi abun alfahari ne, kuma ya yi kira ga al'umma da su kauce ma karkatar da takin zuwa hanyar da bai dace ba domin kauce ma fushin hukuma.
Shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin jihar Katsina Hon. Rabo Tambaya, ya yi jawabin godiya a madadin ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin, inda ya bayyana jin daɗin shi ganin yadda gwamnan ya yi abun da zai taimaki noma a jihar Katsina, yace samar da takin zamanin a lokacin da ya dace abu ne da zai taimaki manoman jihar Katsina.
Shima a nashi jawabin shugaban kamfanin takin zamani na Boko "Boko Fertilizer" Muhammad Sambo Alhassan, ya jinjinawa gwamna Raɗɗa bisa samar da takin zamanin ga al'ummar jihar Katsina bisa farashi mai sauƙi, ya kuma ce samar da takin zai bunƙasa noma, tattalin arziki, da samar da aikin yi a jihar Katsina.
Wanda suka halarci taron akwai Kakakin majalissar dokoki wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin noma na majalisar, shugaban ma'aikatan gidan gwamnati Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, sakataren gwamnan Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, ƴan majalissar zartaswa, da sauransu