AD Saude ya ķara ķaddamar da rabon kayan karatu ga đaluban Primary su dubu đaya 1000 daga mabam-bantan Makarantu guda 24 dake a ķaramar hukumar Katsina.
Sudai wađannan Đaluban an zakulo su ne daga Mazabu 12, da muke da su a ķaramar hukumar ta Katsina.
Shugaban Kwamitin Ilimi, Malam Isma’il Tukur Taury, ya bayyana yadda aka tsara shirin.
Kayan karatun da aka raba sun hađa da Littattafai guda 1000 da Jikkunan 'yan Makaranta suma guda 1000 tare da kwalayen Alli wanda kowane kwali akwai fakiti guda 20 a ciki, daga ķarshe sai akwattan agajin gaggawa (First aid box), wađanda suma adadin su ya kai su 30 suma kuma cike suke da magunguna kala-kala a cikin su. A matakin sakandare kuwa, an bayar da tallafin karatu ga dalibai 48 wanda zai dauki nauyin karatunsu har zuwa kammalawa a shirin farko. Baya ga haka, dalibai 222 daga makarantu na Community School sun amfana da kayan karatu da tallafin sufuri.
Shugaban Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Katsina, Dr. Aminu Tsauri, ya yabawa shirin, yana mai kwatanta shi da hangen nesan Gwamna Dikko Umar Radda. Ya kuma bayyana cewa hukumar ta ware makudan kudade domin tallafawa dalibai, har da tura wasu zuwa kasashen waje domin karatu.
Haka zalika, dan majalisar dokokin jihar Katsina, Hon. Ali Abu Albaba, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su shiga cikin harkar tallafawa ilimi. Fitaccen dan siyasar Katsina, Alhaji Ido Kwado, ya tabbatar da goyon bayansa ga wannan shiri, yana mai bayyana shi a matsayin wata babbar dama ga al’umma.
Kungiyoyi kamar su Dikko Project, Lamido Foundation, da Gwagware Foundation sun bayar da tallafi domin kara wa shirin kuzari tare da saukaka zirga-zirgar dalibai.
Taron ya kasance kashi na uku cikin shirye-shiryen tallafin ilimi da Isah ya gudanar, wanda ya kara tabbatar da jajircewarsa wajen gina al’umma mai ilimi a karamar hukumar Katsina.
Wannan taron ya gudana ne a Kambarawa Primary school dake kan babban titin zuwa Daura, cikin garin Katsina.
Mai girma uban taro Isah Miqdad yayi kira ga đalubai da Malaman da zasu amfana da wannan tallafin da suyi amfani da shi ta hanyar da ta dace, domin ta hakan ne suma zasu amfani al'umma nan gaba.
Daga ķarshe Miqdad ya yaba ma al'ummar da suka halarci taron maza da mata musamman manyan baķi wađanda suka hađa da Abu Ali Albaba, Alhaji Idi Kwado (Sarkin Aiki), Alhaji Musa Gafai, Alhaji Dahiru Danmarna, Alhaji Lolo Dakare da sauransu.